Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kudirin dokar kafa rundunar tsaro mallakin jihar Kano.
Hakan ya biyo bayan zaman da kwamitin majalisar ya yi karkashin jagorancin shugaban ta Alhaji Jibrin Falgore na jam’iyyar NNPP mai wakiltar karamar hukumar Rogo.
Bayan tattaunawa a zaman majalisar sun amince da yiwa dokar karatu na 3 kamar yadda magatakarda ya gabatar.
Jim kadan bayan zartar da kudirin dokar, shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Lawan Husseini na jam’iyyar NNPP mai wakiltar karamar hukumar Dala, ya bayyana cewa an zartar da kudirin ne bayan gudanar da ayyukan da suka dace a kan ta.
Dan majalisar ya bayyana cewa rundunar za ta kasance wata kungiya ce ta al’umma da za ta hada da ayyukan sauran hukumomin tsaro a jihar, kuma za ta inganta harkokin tsaron cikin gida a jihar sosai.
Karin karatu: Majalisar dattawa ta yi wa kwamitoci garambawul, ta nada sabbin shugabanni
Ya kuma bayyana wajabcin kafa jami’an tsaro na jihar, inda ya kwatanta da jihohin kudancin Najeriya, kamar wadanda suka kafa Amotekun, domin karfafa tsaron cikin gida.
A cewarsa, za a baiwa jami’an tsaron izinin daukar makamai kamar yadda doka ta tanada, tare da ba su hurumin kamo wadanda suka aikata laifin tare da mika su ga ‘yan sanda domin gurfanar da su gaban kuliya.
Husseini ya ci gaba da cewa, ma’aikatan da za a dauka ba za su yi alaka da kowace jam’iyya ta siyasa ba.
Shugaban masu rinjaye ya kara da cewa babban kwamandan rundunar da za a nada, dole ne ya kasance mutum mai gaskiya yayin da za a samu kwamandan da zai jagoranci jami’an rundunar a kowace karamar hukuma guda 44 da ke jihar.
Ya ce dole ne babban kwamandan ya kasance jami’in tsaro na Soja ko ‘Yan Sanda mai ritaya wanda ya shafe shekaru akalla 25 yana aiki ba kasa da mukamin Kanar ko Kwamishinan ‘yan sanda ba. (NAN)