Zamfara: Dalibai 17 sun mutu sakamakon tashin gobara

Dead Bodies 675x430 (1)

Wani ibtila’i ya afku a karamar hukumar Kaura-Namoda ta jihar Zamfara, yayin da wata gobara da ta tashi a makarantar Islamiyya tare kashe rayukan Almajirai akalla 17.

Shaidun gani da ido sun ce gobarar ta tashi ne a daren ranar Talata kuma ta ci gaba da ci na tsawon sa’o’i uku, inda dalibai 17 suka mutu, wasu 16 kuma suka jikkata.

Wani mazaunin yankin mai suna Abdulrasaq Bello Kaura ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa musabbabin gobarar sun hada da wasu sanduna da aka ajiye a yankin da ake kira kara.

Labari mai alaƙa: Gobara ta kone gidan kakakin majalisar Zamfara

“Haka ya faru ne a Makaranta Mallam Ghali, cikin dakin karatunsu, kimanin su 100 ne a gidan, bayan sun kwashe daliban, sai suka yi tunanin babu ko daya daga cikinsu da ya rage a cikin gidan, a lokacin da suka dawo bayan gobarar, sai suka fara ganin kafafuwansu, hannayensu, sun kone ba a iya gane su,” inji majiyar.

Ya kara da cewa an yi jana’izar daliban 17 da suka mutu yau Laraba.

Da yake magana ta wayar tarho shugaban karamar hukumar Kaura-Namoda, Kwamared Mannir Mu’azu Haidara ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya bayyana cewa yana kan hanyarsa ta zuwa wurin kuma zai yi karin bayani daga baya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here