Hukumar NAFDAC ta magantu kan taliyar Indomi mai ɗanɗanon kayan lambu

Indomie (1)

Hukumar kula da abinci da magunguna ta ƙasa NAFDAC ta nemi al’umma su kwantar da hankalin su game da wata sanarwar janye Indomie noodles mai ɗanɗanon kayan lambu, inda ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa wannan samfurin ba a yi rajistarsa ba kuma ba a sayar da shi a ƙasar nan.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar a ranar Lahadi, inda ta ce hukumomin lafiya na ƙasar Faransa ne suka fara matakin janye samfurin, kuma lamarin bai shafi Indomie noodles da ake sarrafawa ko aka amince da su domin sayarwa a Najeriya ba.

Hukumar ta ƙara da cewa dandalin kare lafiyar masu saye na ƙasar Faransa mai suna Rappel Conso ne ya sanar da janye samfurin, bayan gano wasu sinadarai da ba a bayyana su ba, wato madara da ƙwai, a cikin Indomie noodles mai ɗanɗanon kayan lambu, lamarin da ka iya jefa masu rashin jituwa da waɗannan sinadarai cikin barazanar lafiya mai tsanani.

Sanarwar, wadda Babbar Darakta-Janar ta hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye, ta sanya wa hannu, ta jaddada cewa samfurin da ake magana a kansa bai fito daga Najeriya ba kuma ba a yi masa rajista da hukumar ba.

Hukumar ta kuma tunatar da cewa taliya na daga cikin kayan da gwamnatin tarayya ta haramta shigo da su daga ƙasashen waje, abin da ya sa shigo da irin wannan samfur a Najeriya bai bi ƙa’ida ba, kuma hakan yana rage yiwuwar samfurin da aka janye ya shiga kasuwannin ƙasar.

A matsayin kariya, NAFDAC ta ce ta ƙarfafa sa ido a faɗin ƙasar domin hana yiwuwar shigowar samfurin da aka janye.

Hukumar ta umarci daraktocin shiyyoyi da masu kula da jihohi da su kasance cikin shiri tare da cire samfurin daga kasuwa idan aka gano shi a kowane yanki, yayin da aka sanya sashen binciken tashoshin jiragen ruwa cikin tsauraran matakan sa ido.

Hukumar ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa dukkan Indomie noodles da aka yi wa rajista domin sayarwa a ƙasar ana sarrafa su ne a cikin gida, kuma ana amincewa da su ne kawai bayan sun cika tsauraran ƙa’idojin tsari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here