Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya kammala shirye-shiryen raba buhunan taki 53,040 ga manoma da sauran masu amfana a fadin kananan hukumomi 13 na yankin Kano ta Arewa gabanin kakar noma ta 2026.
Shirye-shiryen tallafin, wanda ya kunshi manyan motoci 88 na taki, ana sa ran za a fara ranar 31 ga Mayun 2026.
Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Mai Bashi Shawara na Musamman kan Yada Labarai, Malam Ismail Mudashir, ya fitar a ranar Asabar.
A cewar sanarwar, rabon takin na shekara-shekara wani bangare ne na kokarin Barau na tallafa wa manoma, habaka aikin nona, da ba da gudummawa ga samun isasshen abinci a fadin kasar.
Wadanda za su amfana sun hada manoma, masu ruwa da tsaki na jam’iyya, zababun shugabannin kananan hukumomi, mataimaka, kansiloli, da sakatarori a fadin yankin.
Sauran da aka lissafa a matsayin masu amfana su ne mambobin caucus na APC, limamai, sarakunan kauyuka, shugabannin unguwanni, malamai, shugabannin makarantu, jami’an tsaro, da masu tasiri a kafafen sada zumunta.
Barau ya ce samun kayan noma kan lokaci yana da matukar muhimmanci wajen habaka yawan amfanin gona da tabbatar da isasshen abinci.
“Wannan tallafi na nufin tallafa wa manomanmu da kuma taimakawa kokarin Shugaba Bola Tinubu wajen cimma burin samun isasshen abinci a kasa,” in ji shi.
Sanatan ya bukaci wadanda za su amfanan da su yi amfani da takin yadda ya kamata domin cimma manufar habaka aikin gona a lokacin noma na bana.
Ya sake nanata manufarsa kan shirye-shirye da ayyukan da ke da nufin inganta rayuwar al-umma a fadin yankin Kano ta Arewa.











































