Gobara ta kone gidan kakakin majalisar Zamfara

Fire marlet 1

Wata gobara ta kone gidan kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Alhaji Bilyaminu Moriki da ke Gusau.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran majalisar, Bello Madaro ya fitar a Gusau ranar Lahadi

Madaro ya ruwaito magatakardan gidan, Mahmud Aliyu, yana bayyana bala’in a matsayin abin takaici.

Aliyu ya ce gobarar ta lalata kadarori na miliyoyin Naira duk da cewa ba a yi asarar rayuka ba.

Ya ce, “Mahukuntan majalisar dokokin Zamfara sun kadu matuka kan gobarar da ta auku a ranar Lahadin da ta gabata da ta kone gidan kakakin majalisar da ke Gusau.

Madaro ya ce magatakardan na cewa, “A madadin ‘yan majalisar da daukacin ma’aikatan majalisar, ina jajantawa shugaban majalisar da iyalansa bisa wannan bala’i.”

Aliyu ya bukaci shugaban majalisar da iyalansa da su dauki lamarin a matsayin wani aiki na Ubangiji da ya kaddara.

Ya kuma roki Allah da ya kawar  da sake aukuwar bala’in.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here