Ana fargabar mutuwar wasu Sojoji hudu da ke barikin Myoung a unguwar Shomolu a jihar Legas, yayin da wasu suka jikkata bayan da wani direban mota da ake zargin a buge yake ya kutsa ta kansu.
Lamarin ya faru da sanyin safiyar Juma’ar nan, a lokacin da sojojin ke motsa jiki, lamarin da ya jefa sauran sojojin cikin firgici.
Guda daga cikin sojojin da suka tsira wanda aka sakaya sunansa ya bayyana cewa motar tana dauke da wasu matasa uku da ake zargin masu yin damfara ne ta Internet wadanda aka fi sani da ‘Yahoo Boys.
Karanta har ila yau: Jami’an ‘yan sanda 5 sun mutu, 11 sun jikkata a wani hadarin mota da ya rutsa da su a Kano
Ya kara da cewa, motar ta kutsa cikin sojojin ne a kusa da sansanin motsa jiki na soja da ke Myoung Barracks, wanda hakan ya sa daya daga cikin mutanen da ke cikin motar ya gudu a nan take, yayin da sauran biyun kuma aka kama su, aka yi musu dukan tsiya, tare da lalata motarsu.
Sojan ya kuma ce “lokacin da lamarin ya faru kwai jini a ko’ina”.













































