Hukumar JAMB ta sauya ranar jarrabawar UTME

JAMB, UTME, gargadi, jarrabawa, dalibai, yanar gizo, boge
Hukumar JAMB da ‘yan sanda sun gargadi masu jarrabawa da ke shirye-shiryen jarrabawar gama-gari ta 2024 (UTME) da su kula da shiga shafukan yanar gizo na...

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan JAMB ta sanar da ranar Litinin, 3 ga watan Fabrairu a matsayin ranar rubuta jarrabawar UTME maimakon Juma’a 31 ga Janairu kamar yadda aka tsara tun farko.

Dakta Fabian Benjamin shi ne mai magana da yawun hukumar ta JAMB da kuma hulda da jama’a shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a.

Benjamin ya ce canjin ya zama dole domin baiwa hukumar damar aiwatar da muhimman gyare-gyare ga tsarin yin rijistartar jarrabawar.
Jami’ar KWARA ta yi martani kan dakatarwar ilimin shari’a da JAMB tayi

“Wadannan gyare-gyaren sun zo ne dangane da dakatar da wasu shirye-shiryen ilimin shari’a da aka yi kwanan nan a wasu jami’o’i, kamar yadda majalisar kula da ilimin shari’a ta mika wa hukumar”.

“Bugu da ƙari, Hukumar ta gano cewa wasu cibiyoyin gwajin na’urar kwamfuta (CBT) sun yi amfani da kayan aikin yaudara don a amince da su, wanda hakan ya sa ake buƙatar ƙarin bincike da gyara ta hanyar kin amincewa da irin waɗannan cibiyoyin”.

A cewarsa “Hukumar ta nuna damuwa kan yadda irin wadannan cibiyoyi ka iya haifar da rashin nagartattun dalibai da kuma kawo cikas ga masu ruwa da tsaki don haka take neman mafita”.

Ya kara da cewa za a yi amfani da karin lokacin ne domin tabbatar da cewa an yi duk wasu sauye-sauyen da suka dace domin gudanar da rijistar lami lafiya. (NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here