Cibiyar Wole Soyinka Centre for Investigative Journalism (WSCIJ) za ta shirya wani taron yan jaridu, masu binciken kwakwaf, mai taken “AI, Free Press, and Civic Space: Tools, Challenges, and Future of Investigative Reporting” a ranar Laraba, wanda yai dai dai da 30 ga Oktoba, 2024, a Abuja.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da shugaban cibiyar, Motunrayo Alaka, ta fitar ranar Litinin.
Sanarwar ta ce taron zai hada, yan jaridu, shuwagabanni da masana don tattaunawa kan tasirin amfani da fasahar zamini domin gabatar da aikin jarida, musamma wanda ya shafe binkicen kwa-kwaf, dokokin watsa labarai, ƙa’idodi, ‘yancin faɗar albarkacin baki, da kuma rawar da fasaha zamani ke takawa wajen haɓaka gaskiya da riƙon amana, da kuma Sauran mahimman batutuwan.
A gun taron, cibiyar za ta kaddamar da wani shiri mai taken”Journalism and Civic Space” kasha na biyu, Shirin za sa ido kan kafofin watsa labarai, da yadda kafafen yada labarai ke kare sirrin jama’a.
Taron wani ɓangare ne na shirin cibiyar, wanda aka ƙaddamar a cikin shekarar 2021 don tallafawa ‘yan jarida da horar da su, wanda Ofishin Jakadancin Netherlands ya dauki nawin sa tare da haɗin gwiwar cibiyar Centre for Journalism Innovation and Development.