Wani tsohon golan kungiyar Green Eagles na Najeriya Peter Fregene ya rasu.
Segun Odegbami, babban aminin Fregene kuma tsohon dan kwallon duniya ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a Facebook a daren Lahadi.
Odegbami ya ce fitaccen dan wasan kwallon kafar Najeriya ya mutu a gaban Tina, matarsa, da ’ya’yansa biyu bayan doguwar jinya.
Tsohon dan wasan mai shekaru 72, wanda a kwanakin baya ya nemi taimakon kudi ga Fregene, mai shekaru 77, ya nuna godiya ga wadanda suka goyi bayan tsohon mai tsaron ragar a lokacin rashin lafiya.
“Kuma Mutumin ya mutu. ‘Yan mintoci kadan da suka gabata, Peter ‘Apo’ Fregene, OLY, tsohon mai tsaron gida na kungiyar Green Eagles ta Najeriya, wanda ya kasance yana tallafawa rayuwa tsawon mako guda, ya mutu don ganawa da mahaliccinsa,” ya rubuta.