Kaduna: Dan tsohon gwamna Makarfi ya rasu a hatsarin mota

Faisal Makarfi

Dan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Faisal Ahmed Mohammed Makarfi, ya rasu a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a ranar Asabar.

Ya rasu ne a hanyar Kaduna zuwa Zaria a yammacin ranar Asabar, kamar yadda wata majiya ta bayyana.

“Hatsarin ya faru ne a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya da yammacin yau. An kai shi wani asibiti da ba a bayyana ba inda aka tabbatar da rasuwarsa. Mahaifinsa yana asibiti; An kai gawarsa gida domin yi masa jana’iza,” inji majiyar.

Marigayin ya kasance injiniya ne, ya halarci makarantar Kaduna International School kafin ya wuce Kwalejin Adesoye da ke Offa a Jihar Kwara don yin karatunsa na sakandare. Ya kasance a Jami’ar Greenwich, London, don karatun digiri na biyu. Har zuwa rasuwarsa, ya kasance dalibin digiri na uku a Jami’ar Greenwich.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here