Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja zuwa birnin Paris da ke ƙasar Faransa a wata ziyara ta ƙashin kai.
Mai baiwa Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga a shafinsa na X, ya ce Tinubu zai tafi Paris ɗin ne gabanin tafiyar da zai yi zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha domin taron ƙungiyar hadin kan Afirka ta AU.
A birnin Addis Ababa wanda ake sa ran zai isa a farkon mako mai zuwa, Shugaba Tinubu zai haɗu da shugabannin ƙasashen Afirka domin taron ƙungiyar da za a gudanar daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Fabrairun 2025.
A yayin ziyarsa zuwa Faransa, Tinubu zai haɗu da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron.












































