Gobara ta ƙone wasu ƙauyuka uku a Jigawa

1678100704775
1678100704775

Wata mummunar gobara da ta tashi a wasu ƙauyuka uku a cikin ƙaramar hukumar Kiyawa a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ta janyo asarar dukiyoyi masu yawa.

Gobarar ta yi sanadin ƙonewar ɗaruruwan gidaje da amfanin gona da kuma dabbobi masu yawa.

Al’amarin ya auku ne ranar Lahadi da rana a ƙauyukan Malamawa da Karangiya da kuma Kwaleji.

Mutanen ƙauyukan sun kwana a bayan gari saboda gobarar ta ƙone musu gidajensu.

Rahotonni sun ce an kwashe lokaci mai tsawo kafin a iya kashe wutar sakamakon iskar da ke kaɗawa a kauyukan.
(BBC)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here