Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gayyaci kamfanin matatar mai ta Dangote da kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (NUPENG) zuwa taron gaggawa a yau Juma’a, sakamakon taƙaddama da ta kunno kai kan zargin karya yarjejeniyar da aka cimma kan ‘yancin ma’aikata su shiga kowace kungiya da suka ga dama.
Taron zai gudana da misalin karfe uku na rana tare da halartar shugabannin NLC da sauran masu ruwa da tsaki.
Labari mai alaƙa: NUPENG ta yi barazanar komawa yajin aiki, bayan da ta zargi Dangote da karya yarjejeniya
A ranar 9 ga Satumba, Dangote da NUPENG sun sanya hannu kan yarjejeniya a hedikwatar DSS a Abuja, inda aka amince cewa dukkan ma’aikata na da ‘yancin shiga kowace kungiya. Shaidun taron sun hada da shugabannin NLC, TUC da ministoci.
Sai dai NUPENG ta zargi kamfanin da karya yarjejeniyar tun bayan kwana guda, inda ta ce an tilasta cire tambarin NUPENG daga kan motocin dakon mai tare da maye gurbinsu da na wata kungiyar da ake kira DTCDA wadda













































