Abdulmumin Jibrin ya amince da korarsa daga jam’iyyar NNPP

Abdulmumin Jibrin

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana mamakinsa kan yadda jam’iyyar NNPP ta kori shi daga cikinta.

Jam’iyyar ta sanar da hukuncin ne ta bakin shugaban ta na Kano, Hashimu Dungurawa, inda ta zarge shi da aikata abin da ya saba wa manufar jam’iyya da kuma kasa biyan kuɗin da ya rataya a kansa.

A cikin wata sanarwa da Jibrin ya fitar da kansa, ya ce abin ya zo masa a matsayin babban mamaki, domin maganganun da ya yi a hirarrakin da aka yi da shi bai kamata su kai ga hukuncin kora ba.

Ya ƙara da cewa ya tsaya kan dukkan kalaman da ya yi, yana mai cewa jam’iyyar ta yi watsi da hakkinsa na ba shi damar kare kansa.

Labari mai alaƙa: Da ɗumi-ɗumi: Jam’iyyar NNPP ta kori Abdulmumin Jibrin

Jibrin ya nuna cewa da jam’iyyar ta bi matakan da suka dace na adalci, da ba a kai ga korarsa ba, duk da haka, ya amince da hukuncin da aka ɗauka a kansa, yana mai cewa ya karɓi wannan mataki ba tare da jin haushi ba saboda girmamawa ga jam’iyyar da mambobinta.

Dangane da zargin kin biyan kuɗi, Jibrin ya roƙi jam’iyyar da ta aika masa da cikakken lissafin abin da yake biya, ya ce zai biya nan take, domin bai taɓa yin watsi da biyan kuɗin jam’iyya ba, ya kuma roƙi jam’iyyar da ta guji kai shi kotu da kuma tsokanar juna ta hanyar zagi ko cin mutunci.

Ya gode wa jam’iyyar bisa goyon bayan da ya samu a lokacin da yake cikinta, tare da bayyana cewa yana kira ga magoya bayansa su mara masa baya a sabon tafiyar siyasa da zai sanar nan gaba, sai dai ya ce ba ya da wata matsala da waɗanda za su zauna a NNPP, domin zai ci gaba da kyakkyawar mu’amala da su.

A ƙarshe, Jibrin ya bayyana cewa zai yi nazari sosai kan matakin siyasa da zai ɗauka a gaba, yana mai cewa ya bar komai ga taimakon Allah.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here