Hukumar NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane 231, sama da 600 sun ji rauni sakamakon ambaliyar a 2025

MOKWA FLOODING

Hukumar ba da agajin G’gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta tabbatar da cewa ambaliyar ruwa a 2025 ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 231, ta jikkata 607, tare da shafar fiye da mutane 315,000 a faɗin ƙasar nan. Haka kuma, mutane 114 sun bace yayin da lamarin ya shafi ƙananan hukumomi 86 a jihohi 25.

Binciken hukumar ya nuna cewa mutane 113,367 sun rasa matsugunansu, gidaje 40,493 sun lalace, yayin da gonaki 46,304 suka salwanta.

Rahoton NEMA ya nuna jihohi goma da suka fi fuskantar illa sun haɗa da Legas, Adamawa, Akwa Ibom, Imo, Taraba, Rivers, Delta, Abia, Borno da Kaduna.

An bayyana cewa yara ne suka fi fuskantar matsalar, inda rahoton ya nuna yara 143,683 aka shafa, mata 100,079, maza 60,408, tsofaffi 11,592 da nakasassu 2,265. Jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Borno, Delta, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Kwara, Legas, Neja, Ondo, Rivers, Sokoto da Abuja.

Labari mai alaƙa: Ambaliyar ruwa ta tilasta rufe Masallacin Juma’a mai shekaru 40 a garin Kankia

NEMA ta ce babban ƙalubalen da aka fuskanta bayan ambaliyar ya haɗa da ƙarancin kayan aiki wanda ya kai kaso 69%, matsalar rashin samun damar isa wuraren da abin ya shafa 16%, rashin haɗin kai daga al’umma 7% da kuma barazanar tsaro 6%.

A cewar hukumar, abubuwan da ake buƙata mafi gaggawa sun haɗa da abinci, mafaka, tsaftar ruwa da muhalli, kiwon lafiya, hanyoyin dogaro da kai, abinci mai gina jiki, ilimi, kariya da kuma tsaro

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here