Aliyu Gusau ya janye daga takarar gwamnan Zamfara

aliyu deputy
aliyu deputy

Alhaji Mahdi Aliyu Gusau, tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya janye daga takarar.

Aliyu Gusau ya bayyana hakan ne a yau Laraba a Gusau sa’o’i kaɗan da fara gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamnonin jam’iyyar.

Ya bukaci magoya baya da wakilansa da shugabannin jam’iyyar su zabi Dakta Dauda Lawal-Dare domin ya samu tikitin takarar gwamna a zaɓen fidda gwani.

Aliyu-Gusau ya godewa magoya bayansa kan irin ɗimbin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake mataimakin gwamnan jihar da kuma bayansa.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa ƴan takara uku da suka haɗa da Lawal-Dare, Alhaji Abubakar Nakwada da Alhaji Wadatau Madawaki ne ke karawa a zaben fidda gwanin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here