Ƴan Majalisar Kano 4 sun Koma APC daga NNPP

kano assembly new 1 1
kano assembly new 1 1

Ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazabar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, watau Madobi Kabiru Yusuf Isma’il, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC.

Solacebase ta kawo rahoton sauya sheƙar mataimakin shugaban majalisar dokokin ta Kano, Zubairu Hamza Massu zuwa NNPP da kuma wasu ‘yan majalisa uku da suka hada da Abdullahi Yaryasa wakilin Tudun Wada, Muhammad Butu-Butu mai wakiltar Tofa, Rimin-Gado da kuma Kabiru Ismail wakilin ƙaramar hukumar Madobi.

Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai Malam Muhammad Garba ya fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dawakin Kudu Mu’azzam El-Yakubu ya fice daga jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso zuwa APC.

Sanarwar ta ce a kwanakin baya guguwar sauya sheƙa ta mamaye jam’iyyar NNPP, musamman ‘yan majalisar jiha da na ƙasa.

“Tuni dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar Bagwai da Shanono, Isa Ali ya koma APC kwanaki bayan ya koma jam’iyyar NNPP,” in ji sanarwar.

‘’ Shi ma ɗan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Dambatta, Murtala Kore ya yi bara’a da zama ɗan jam’iyyar NNPP ya ci gaba da zama a APC.’’

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here