Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC, tace kusan Yan Nijeriya Miliyan 38 ne ba zasu sami damar Kada kuri’a a Babban zaben shekarar 2023 ba.
Shugaban Hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya bada wannan sanarwar yayin da yake zantawa da manema Labarai a ranar Laraba.
Yakubu, yace kusan kaso 45 cikin 100 na mutanen da suka yi rijistar Katin zabe, bata yiwu ba saboda haka hukumar ba zata sanya su cikin rijistar wadanda zasu yi Zabe a Shekara 2023 ba.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa tun a shekarar 2019 mutane miliyan 84 da dubu 4 da 84, suka yi rijistar a fadin Najeriya.
Akwai karin bayani nan gaba………..












































