Mutum 26 sun Mutum bayan da Jirgin ruwa ya yi Hatsari a Sokoto

boat 600x381 1
boat 600x381 1

Mutane 26 aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da ake ci gaba da neman wadanda suka bace, bayan da wani jirgin ruwa ya kife a cikin kogin Shagari dake karamar Hukumar Shagari ta Jihar Sokoto.

Shugaban Yankin Shagari Alhaji Aliyu Dan-Tani wanda shi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga kamfanin dillancin Labarai na Kasa NAN, a ranar Laraba yace, hatsarin ya faru ne tun da yammacin ranar Talata.

Dantani, yace a cikin mutane 26 da aka samu gawarwakinsu 21 cikinsu Mata ne yayin da sauran mutum 5 din kuma Kananan Yara ne.

Ya kara da cewa har kawo yanzu ba a tabbatar da adadin Fasinjojin dake cikin jirgin ba, yayin da ya yi hatsarin.

A cewar sa yanzu haka dai direbobin Kwale-kwale na ci gaba da duba cikin Kogin don samo sauran gawarwakin da suka rage a ciki tare da tseratar da wasu idan ba su mutu ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here