Gwamnatin tarayya ta tabbatar da tserewar fursunoni 600 daga gidan gyaran hali na Kuje da ke birnin tarayya Abuja, sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai gidan a ranar Talata.
Dr Shuaib Belgore ya ce an kashi jami’in tsaro guda daya, yayin da wasu kuma jami’an suka sami raunika, lokacin da suke maida martani ga ‘yan bindigar.
Ya kuma kara da cewa ‘yan bindigar sun lalata kayan aikin jami’an tsaro yayin kai harin.
Ya kuma ce izuwa yan zu an kama fursunoni 300 da suka tsere daga gidan.













































