DA DUMI-DUMI: Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur

BREAKING
BREAKING

Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur.

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja.

Da take jawabi yayin wani taro da aka gudanar a majalisar dokokin kasar, Ministan ta ce an dakatar da shirin har zuwa wani lokaci.

Taron ya samu halartar Timipre Sylva, karamin ministan albarkatun man fetur; wakilan kamfanonin mai da sauran masu ruwa da tsaki.

Idan za a iya tunawa, Karamin Ministan Man Fetur, Timipre Sylva, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya goyon bayan cire tallafin da ake samu daga Premium Motor Spirit, wanda aka fi sani da fetur.

Sylva ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a wani shiri na gidan Talabijin na Channels.

“Zan gaya muku sarai cewa a halin yanzu, cire tallafin gaba daya ba ya cikin farantinmu,” in ji Sylva.

“Shugaban tarayyar Najeriya baya goyon bayan cire tallafin a wannan lokaci,” in ji shi.

Ministan ya bayyana cewa, wani bangare na dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayya ba ta tunanin cire tallafin man fetur, shi ne illar da zai yi ga ‘yan Najeriya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here