Dakarun rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa da ke aiki a karkashin Sector 3 a garin Mongunu sun kama wani dan ta’adda da ake zargi da kai kayan hada bama-bamai zuwa karamar hukumar Gubio ta jihar Borno.
Wata sanarwa a ranar Juma’a ta bakin babban jami’in yada labarai na rundunar, Lt-Col. Olaniyi Osoba ya ce an kama dan ta’addan ne a ranar Alhamis din da ta gabata biyo bayan hadin gwiwa da MNJTF da Civilian JTF suka yi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Wanda ake zargin mai suna Mista Murktar Alhaji Chari (28) ya amsa laifin kai kayan zuwa garin Damasak da ke karamar hukumar Mobbar domin kai hari kan dakarun MNJTF.