Shirin bunkasa aikin Noma da dakile matsalar kamfar Ruwa a wuraren tsandauri wato ACRESAL ta gudanar da wani gangamin wayar da kan jama’a don aiwatar da shirin sake tsugunar da jama’a (RAP) a yankin Bulbula-Gayawa da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in sa ido da tantance ayyukan ACReSAL na Kano, Aminu Gidado Yusha’u, a madadin kwamishinan muhalli na jiha kuma shugaban kwamitin gudanarwa na jiha Dr. Dahir Muhammad Hashim.
Fadakarwa da nufin sanin mutanen da abin ya shafa (PAPs) da sauran al’umma wanda shine muhimmin sashi na ayyukan da aka tsara na kawar da zaizayar kasa a yankin.

SolaceBase ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kano, a karkashin shirinta na (ACReSAL) da bankin duniya ke tallafawa, ta bayar da kwangilar Naira biliyan 8.5 na aikin kawar da zaizayar kasa a yankin Bulbula/Gayawa.

Shi dai wannan shiri da aka dade ana jira yana da nufin rage illar da zaizayar kasa ta haifar a kananan hukumomin Ungogo da Nassarawa, inda mazauna yankin suka sha fama da matsalar gurbacewar muhalli tsawon shekaru.

Da yake jawabi a wajen taron, Yusha’u ya bukaci al’umma da su ba gwamnati hadin kai don ganin an gudanar da aikin cikin nasara, yana mai jaddada aniyar gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na magance matsalolin muhalli da suka dade suna shafar ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin al’umma.
Haka kuma jami’in kare muhalli Alhaji Mukhtar Bello ya yi tsokaci kan shirin na RAP, inda ya bayyana bukatar hadin kai domin ganin an kammala shirin a kan lokaci da kuma fara ayyukan gwamnati.
A nasa jawabin Hakimin Gama Alhaji Rabi’u Muhammad Isyaku ya yabawa kokarin gwamnati ta hanyar aikin Kano-ACReSAL tare da yin alkawarin bayar da gudummuwar al’umma wajen ganin aikin ya samu nasara.












































