A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Kogi ta ce ta fara wani yunkuri domin kwato kamfanin siminti na Obajana daga rukunin kamfanonin Dangote.
Idan dai za a iya tunawa a ranar Larabar da ta gabata ne aka rufe kamfanin simintin saboda rikicin mallakar kamfani da gwamnatin jihar ke takaddama akai.
Sakatariyar gwamnatin Kogi Uwargida Folashade Ayoade to bayyana hakan a Lokoja, inda ta yi zargin cewa mika kamfanin siminti na Obajana zuwa kamfanonin Dangote lamari ne da “Ba shi da inganci kwata kwata.
Uwargida Folashade cikin rahoton ta bayyana cewa, takardun shaidar mallaka na kamfanin Obajana mallakin gwamnatin jihar Kogi ne, akayi amfani da shi wajen samun lamuni na Naira miliyan dubu 63 daga Dangote.
Ta ce kwamitin bisa la’akari da bincikensa, ya ba da shawara ga jihar ta dauki matakan kwato kamfanin siminti na Obajana daga hannun Dangote.
“An yi amfani da takardu kala uku ne wajen samun lamuni na naira miliyan dubu sittin da uku domin gina kamfanin siminti a Obajana.”
A nasa jawabin, Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya ce ya dauki wannan matakin ne bisa ga damar da doka ta ba shi na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kogi.
Bello ya ce hakan kuma na zuwa ne biyo bayan zanga-zangar da al’ummar jihar suka yi na ganin an mayar da su saniyar ware da rukunin kamfanonin Dangote ta ke mu su.
Gwamnan, ya ce jihar a bude dukkan matakai don tattaunawa da zarar rukunin Dangote ya shirya a tattauna.
Kan halin da ake ciki, kungiyar masana’antun Najeriya ta yi allah-wadai tareda kakkausar suka ga kutsen da jami’an tsaron jihar da ‘yan banga suka kai wa kamfanin siminti na Dangote a ranar Larabar da ta gabata bisa umarnin gwamnan jihar Yahaya Bello.
Kungiyoyin kukada masana’antun sun kara dacewa daukar irin wannan mataki ka iya hana masu sanya hannun jari a jihar.












































