Dalilan dasuka sa Habasha ta jingine cigaba da baiwa ‘yan najeriya biza

Geoffrey Onyeama 1
Geoffrey Onyeama 1

Gwamnatin Tarayya ta ce dakatarwar da kasar Habasha tayi na cigaba da mika Visa alokacin da ‘yan Najeriya ke zuwa kasar tare da matafiya daga wasu kasashe 41, na da nasaba da rashin tsaro.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Mrs Francisca Omayuli ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar kuma aka rabawa manema labarai a Abuja.

Sai dai gwamnatin ta bukaci ‘yan Najeriya da ke da niyyar zuwa kasar Habasha don samun bizar dasuje ofishin jakadancin kasar ko ta hanyar ziyartar hukumar shige da fice da zama dan kasa to wannan adireshi www.evisa.gov.et .

Omayuli ta ce “Hukumomin a kasar Habasha sun bayyana cewa matakin na da nufin inganta iyakoki na zirga-zirgar mutane zuwa Habasha saboda rikicin da ke faruwa a Arewacin kasar,” in ji Omayuli.

Ta kuma bayyana cewa matakin na wucin gadi ne har sai an samu sauyi a harkokin tafida harkokin tsaro a kasar.

Ta kara da cewa ‘yan Najeriya da ke jigila a filin jirgin sama na Bole dake birnin Addis Ababa za su bukaci ingantacciyar bizar shiga don ba su damar shiga otal a birnin.

Ta ce dokar takaita bizar ta wucin gadi ta fara aiki ne a ranar 29 ga watan Satumba, kuma gwamnatin tarayya za ta hada kai da hukumar kula da shige da fice ta kasa da kamfanonin jiragen sama domin tabbatar da wayar da kan matafiya ‘yan Najeriya da ke da niyyar shiga kasar Habasha.

Dagan takuma bayyana damuwar gwamnatin kasar dangane da yadda gwamnatin Habashan ke cin zarafin tsarin bizar kasar.

A cewar hukumomin Habasha da dama wasu ‘yan Najeriya da ke shiga kasar da bizar yawon bude ido na ‘yan kwanaki Amma daga bisani suna cigaba da gudanar da ayyukan da ba su dace ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here