Nuhu Ribadu ya mika Janar Tsiga, Ambasada Yohanna da wasu 17 da aka yi garkuwa da su ha iyalansu

WhatsApp Image 2025 04 03 at 20.20.13 750x500 1 750x430

A ranar Alhamis ne mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya mikawa iyalan Brig.-Gen. Maharazu Tsiga (mai ritaya) da Ambasada Gideon Yohanna, da wasu mutane 17 da aka yi garkuwa da su a Abuja.

An yi garkuwa da Tsiga, tsohon Darakta-Janar na Hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC) ne a ranar 5 ga Fabrairu, 2025, a mahaifarsa ta Tsiga, a karamar hukumar Bakori ta Jihar Katsina, tare da wasu mutane tara, yayin da Ambasada Yohanna, tsohon Mataimakin Shugaban Jakadancin Najeriya a Pretoria, Afirka ta Kudu, aka yi garkuwa da shi a watan Janairu a karamar hukumar Zango Kataf.

Da yake jawabi a lokacin mika su a cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa (NCTC), reshen dake karkashin ofishin NSA, Ribadu ya ce an samu nasarar ceto wadanda aka sace ne sakamakon kokarin da sojoji da sauran jami’an tsaro suka yi.

Hukumar ta NSA ta ce: “Mun yi wasu ayyuka biyu a baya a sakamakon ayyukan dakarun mu da sauran jami’an tsaro, mun samu nasarar ceto tare da dawo da su.

Karanta: Tsohon shugaban hukumar NYSC da aka yi garkuwa da shi ya shaƙi iskar ‘yanci

Ya kuma tabbatar da cewa aikin ceto duk wadanda aka yi garkuwa da su daga hannun wadanda suke yin garkuwa da su wani kokari ne na gwamnatin yanzu. Ya kara da cewa sojoji da sauran jami’an tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun ceto duk wadanda abin ya shafa.

Shugaban hafsan sojin kasa (CDS), Janar Christopher Musa, ya kuma bayar da tabbacin cewa rundunar za ta tabbatar da cewa duk wadanda aka yi garkuwa da su a fadin kasar nan za su sake haduwa da iyalansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here