Kungiyar tsoffin ma’aikata da kungiyar kwadago ta bayyana goyon bayanta ga sauye-sauyen tattalin arzikin da shugaba Bola Tinubu je yi, tana mai cewa farashin kayan abinci ya ragu matuka a fadin kasar nan.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis, shugaban kungiyar na rikon kwarya Kwamared Isa Tijjani, ya amince da matsalar tattalin arzikin da ‘yan Najeriya suka fuskanta a farkon gwamnatin Tinubu amma ya dage cewa kokarin gwamnati ya haifar da ci gaba a zahiri.
Tijjani, wanda tsohon mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa ne kuma tsohon shugaban kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa (NUPENG) ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika banbance ra’ayi mai ma’ana da adawa maras tushe.
Ya nanata cewa yin cudanya da gwamnati cikin mutuntawa da hanyar warwarewa zai haifar da kyakkyawan sakamako fiye da kiyayya.
Tijjani ya kuma yi Allah-wadai da tashe-tashen hankula a jihar Edo a baya bayan nan, yana mai bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na tayar da kayar baya da rashin zaman lafiya a Najeriya.
Ya yi maraba da matakin gaggawar da shugaban kasar da gwamnan jihar Edo suka bayar wajen shawo kan lamarin tare da yin kira da a gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.
Shugaban Kwadagon ya kuma bukaci ‘yan kungiyar da su shiga babban taron Majalisar Zartaswa da za a yi, inda za a bayyana matsayin kungiyar a kan al’amuran kasa da kuma yada su a dukkan matakan gudanar da mulki tun daga jiha zuwa kananan hukumomi da kuma kananan hukumomi.
Gwamnatin Tinubu ta fuskanci suka kan kalubalen tattalin arzikin kasar, da suka hada da hauhawar farashin kayayyaki da faduwar darajar kudi, sai dai kuma jami’an gwamnati sun tabbatar da cewa manufofinsu za su samar da fa’ida na dogon lokaci ga tattalin arzikin Najeriya.