Shahararren malamin addinin musulunci Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya rasu

IMG 20250404 WA0002 710x430

Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Imam Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi rasuwa.

Sheikh Muhammad Kabir Haruna ya tabbatar da rasuwarsa a shafin sa na Facebook a daren Alhamis.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa marigayi Imam babban malamin addinin musulunci ne a nahiyar Afirka, wanda kuma aka san shi da irin gudunmawar da ya bayar wajen yada koyarwar addinin musulunci a fadin nahiyar.

Baya ga aikinsa na ilimi, Imam Idris ya kasance dan kasuwa kuma manomi.

Malamin ya dade yana fama da rashin lafiya, kuma kwanan nan ya tafi kasar waje neman magani a cikin watan Ramadan da ya gabata.

Za a yi jana’izar sa da karfe 10:00 na safiyar Juma’a a Masallacin Idi da ke filin Games Village a Jihar Bauchi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here