Majiya mai tushe daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa mai bawa shugaban kasa Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin siyasa a ofishin mataimakin shugaban kasa Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya mika takardar murabus din sa.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, a ranar Juma’a dai rahotanni suka ce Baba-Ahmed, tsohon kakakin kungiyar dattawan Arewa (NEF) ya mika takardar murabus din sa kimanin makonni biyu da suka gabata.
Sai dai har zuwa lokacin wannan rahoto, babu tabbas kan ko fadar shugaban kasar ta amince da murabus din nasa a hukumance ko a’a.
Duk da yake ba a bayyana dalilan murabus din nasa a bainar jama’a ba, amma masu sharhi na ganin hakan ya samo asali ne daga ra’ayinsa.
Karin karatu: Kungiyar kwadago ta goyi bayan matakin sauye-sauyen tattalin arziki na Tinubu, ta ba da dalilai
Zaman Baba-Ahmed a fadar shugaban kasa bai rasa nasaba da rigima ba. Irin rawar da ya taka, musamman alakarsa da NEF, ya janyo suka daga wasu bangarori, ciki har da karamin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle.
A watan Afrilun 2024, Matawalle ya caccaki wadanda aka nada daga Arewa, wadanda a nasa ra’ayin suka yi shiru a kan sukar gwamnatin Tinubu. An yi ta kallon kalaman nasa a matsayin kakkausar murya ga Baba-Ahmed, biyo bayan karewar da kungiyar ta NEF ta yi bayan da kungiyar ta nuna cewa Arewa ta yi kuskure wajen zaben Shugaba Bola Tinubu a 2023.
Baba-Ahmed dai ya ce maimakon ya kai wa NEF hari, kamata ya yi Matawalle ya mayar da hankali wajen nuna nasarorin da ya samu a gwamnati.
Sai dai Matawalle ya mayar da martani, inda ya nanata cewa duk wanda gwamnati ta nada yana da hakki na inganta gwamnatin da suke yi.













































