Kotun koli ta kori Abure daga matsayin shugaban LP na kasa

BREAKING

Kotun koli ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke na amincewa da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar LP ta kasa.

A wani hukunci daya yanke, kwamitin mutane biyar na kotun koli ya bayyana cewa kotun daukaka kara ba ta da hurumin bayyana Abure a matsayin shugaban jam’iyyar Labour ta kasa, bayan gano tun da farko cewa jigon karar ya shafi shugabancin jam’iyyar ne.

Kotun kolin ta ce batun shugabanci wani lamari ne na cikin gida na jam’iyyar da kotuna ba ta da hurumin shari’a.

Kotun ta kuma amince da karar da Sanata Nenadi Usman da daya suka shigar inda ta ce ya dace.

Har ila yau, ta yi watsi da karar da kungiyar Abure ta jam’iyyar Labour ta shigar kan rashin cancanta.

Karin bayani na nan tafe……

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here