Gobara ta tashi a Jami’ar Northwest Kano, mutum daya ya jikkata

Kano varsity6

Wata gobara da ta tashi a hawa na tara na jami’ar Northwest ta Kano a ranar Alhamis lamarin da ya haifar da jikkatar wani mutum wanda yanzu haka yake kwance a asibiti.

Gobarar wadda ta fi shafar ofisoshin shugaban ma’aikatar da malaman jami’a a sashen fasahar sadarwa (ICT), rahotanni sun ce wutar lantarki ce ta haddasa ta.

An garzaya da wani jami’in tsaro, wanda ya samu horo kan kashe gobara zuwa asibitin jami’ar, bayan da ya shaki hayakin yayin da yake kokarin shawo kan wutar.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa jami’an kashe gobara na hukumar kashe gobara ta jihar Kano da na hukumar kashe gobara ta tarayya sun kai dauki matakin gaggawa wajen kashe ta.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin shugaban hukumar kashe gobara ta Jihar Kano Sani Anas, ya ce an shawo kan lamarin kafin ya kai ga wasu sassan ginin.

Har ila yau, mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, ya ce yayin da aka yi nasarar kashe gobarar, har yanzu ba a kai ga tantance yawan barnar da ta yi ba.

“Ba za mu iya kididdige asarar da aka yi a wannan lokacin ba, amma muna godiya da cewa ba a rasa rayuka,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here