Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe mutum 10 a wasu sabbin hare-hare da suka kai a wasu kauyuka biyar a karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato.
An kai hare-haren ne kwanaki shida bayan wani harin makamancin haka a yankin Ruwi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10, yayin da wasu uku suka samu raunuka.
Shugaban Hukumar Raya Al’adu ta Bokkos (BCDC), Kwamared Farmasum Fuddang, ya tabbatar wa manema labarai kashe-kashen na baya-bayan nan a wata sanarwa da ya fitar a Jos, babban birnin jihar.
A cewarsa, “A cikin mako daya kacal, mun yi asarar al’umma sama da 20 sakamakon ayyukan wadannan makiya, da ba su da wani alheri ga al’ummar jihar.”
Ya ci gaba da cewa, “A ranar 2 ga Afrilu kadai, sun kashe sama da mutane 10. Muna godiya ga rundunar sojin Najeriya da ‘yan sandan da suka yi gaggawar amsa kiran gaggawa, wanda ya taimaka wajen rage hasarar rayuka.
Hare-haren na baya-bayan nan sun tilastawa mazauna yankunan da lamarin ya shafa da makwabtansu tserewa domin tsira da rayukansu.
A halin da ake ciki, Gwamnatin Jihar Filato ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai a kauyukan Mangor Tamiso, Daffo, Manguna (Tagai), Hurti da Tadai na karamar hukumar Bokkos a jihar a daren ranar 2 ga Afrilu, 2025.
Kwamishiniyar Yada Labarai na Jihar, Hon. Joyce Ramnap, wacce ta zanta da manema labarai a wata hira ta wayar tarho, ta kuma roki a kwantar da hankula a tsakanin mazauna jihar.