Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya sallami Kwamishinan Tsaron Ciki da Harkokin Gida, Alhaji Ibrahim Gambo Galadima.
Matakin sallamar ya fara aiki nan take, kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kai, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa matakin wani ɓangare ne na kudirin gwamnatin jihar na sake sauya tsarin majalisar zartarwa lokaci zuwa lokaci domin shigar da sabbin tunani, ƙarfafa shugabanci da kuma sake tsarawa domin inganta ayyukan gwamnati a fadin jihar.
Gwamna Bala Mohammed ya gode wa Ibrahim Gambo Galadima bisa irin gudunmawar da ya bayar wa Jihar Bauchi a lokacin da yake rike da mukamin, tare da yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.
Sanarwar ta kuma tabbatar wa al’ummar Jihar Bauchi cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da nagartaccen shugabanci a jihar.
Haka kuma, sanarwar ta kara da cewa za a sanar da wanda zai maye gurbin Galadima a lokacin da ya dace.













































