Jam’iyyar APC ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta tarbi gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, wanda ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ba a hukumance.
Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na TVC a ranar Lahadi, inda ya ce jinkirin wani bangare ne na dabarun siyasa da jam’iyyar ke bi domin la’akari da yanayin yankuna daban-daban, musamman jihohin arewa.
Ya bayyana cewa jam’iyyar na shirin farawa da Jihohin Arewa ne saboda kusantowar watan Ramadan, ganin cewa mafi yawan al’ummar yankin Musulmi ne.
Ya ce akwai al’ummomi da dama a Arewa da ke da matuƙar damuwa da lamuran da suka shafi Ramadan, don haka jam’iyyar ta ga dacewar farawa da shugabannin Arewa kafin komawa Kudancin ƙasar inda batun Ramadan ba ya da irin wannan tasiri.
Yilwatda ya jaddada cewa wannan mataki ba ya nufin Siminalayi Fubara ba shi da iko ko tasiri a jam’iyyar, yana mai cewa matakin dabarar siyasa ne kawai da kuma mutunta yanayin kowace al’umma.
Dangane da tambayar da aka yi masa cewa ko Fubara na fuskantar ƙalubale wajen jagorantar APC a Jihar Rivers, Yilwatda ya ƙalubalanci wannan ra’ayi, inda ya ce babu wani ƙorafi ko takardar koke da aka miƙa masa a hukumance daga kowanne ɓangare.
Ya kuma bayyana cewa ƙungiyoyin goyon baya ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ke aiki a Jihar Rivers ba su da alaƙa kai tsaye da tsarin jam’iyyar APC, yana mai cewa ayyukan jam’iyya suna tafiya ne ta ofisoshin da aka tanada a hukumance.
Rikicin siyasar da ke kewaye da jagorancin Fubara ya samo asali ne daga rikicin da ya dade yana gudana a Jihar Rivers, bayan dangantakarsa da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, ta lalace sakamakon rikicin iko bayan zaɓen 2023, lamarin da ya kai ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ayyana dokar ta-ɓaci na watanni shida a jihar.
Siminalayi Fubara ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar 9 ga Disamba, 2025, matakin da ake ganin yana da alaƙa da shirin neman shirin neman wa’adi na biyu a 2027 da kuma ƙoƙarin ƙarfafa goyon baya bayan rikicinsa da Wike.
Duk da cewa Wike ya ci gaba da kalubalantar ikirarin cewa sauya sheƙar Fubara kai tsaye ya mayar da shi shugaban jam’iyyar APC a jihar, lamarin da ya ƙara tsananta rikicin siyasa tsakanin ɓangarori a APC da PDP a Jihar Rivers gabanin zaɓen 2027.













































