Mataimakin Shugaban APC Na Kasa, Salihu Lukman Ya Yi Murabus 

Salihu Moh. Lukman 750x430
Salihu Moh. Lukman 750x430

Mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a Arewa maso yamma, Salihu Mohammed Lukman, ya yi murabus daga kujerarsa.

Lukman, wanda ya kasance mamba a kwamitin aiki na APC, ya bayyana cewa ya yi murabus ne saboda yanayin abubuwa a jam’iyyar mai mulki wanda ya saba da manufar kafa jam’iyyar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai kwanan watan 26 ga watan Yuli, kuma ya aika wa mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abubakar Kyari.

Ya ce zai zama kisan kai da kai maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu, tsohon shugaban jam’iyyar mai mulki na kasa da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje.

Tun farko dai mun ji cewa Salihu Lukman ya rubuta takarda zuwa ga gwamnonin da ke mulki a jam’iyya mai-mulki.

Lukman ya aika wasika zuwa ga Gwamnan jihar Imo, yana gargadi kan yin adalci game da wanda zai zama shugaban APC, inda ya ce ya kamata gwamnoni su zama tamkar kwakwalwar jam’iyyar mai mulki a halin da ake ciki.

Kafin gwamnonin su cin ma matsaya, mataimakin shugaban na APC ya ce ya kamata a fara zama da NWC a game da wanda zai jagorance su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here