Gwamnatin tarayya ta fadawa kungiyar kwadago cewa aniyar ta na shiga yajin aiki sakamakon tsadar man fetur ba ya bisa ka’ida.
Idon za ku iya tunawa dai kungiyar kwadago ta bawa gwamnatin tarayya wa’adin sati daya data sake duba wasu tsare tsare data bullo dasu, ko kuma kungiyar ta shiga yajin aiki.
Sai dai kuma sakataren ma’aikatar shara’a ta kasa B.E Jedy-Agba a ranar Laraba ta ce yin yajin aikin ya karya doka, saboda kotun ma’aikata ta hana yin yajin aiki akan cire tallafin man fetur.
Ta kara da cewa tuni kotu ta bada umarni a ranar 5 ga watan Yuli cewa kada kungiyar kwadago da kuma wata kungiya su shiga yajin.













































