Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani mutum mai suna Usman Sagiru, mai shekaru 20, dan unguwar Sharifai Quarters, da laifin kisan kai da kuma kai wa ‘yan banga hari da ya afku a tawagar Sarki Sanusi Lamido Sanusi II bayan sallar idi a ranar Lahadi, 30 ga Maris, 2025, da misalin karfe 12:40 na rana.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce, Usman Sagiru da wasu sun caka wa Surajo Rabiu, dan banga daga unguwar Sabon Titi Jaba Quarters wuka, wanda daga baya ya mutu sakamakon raunukan da ya samu.
“Wani dan banga, Aminu Suleman daga Kofar Mata Quarters, ya samu raunuka kuma a halin yanzu yana jinya a Asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano, a yayin da suke bada garkuwa ga Sarki Sanusi, inji sanarwar.
Rundunar ‘yan sandan ta fara gudanar da bincike kan lamarin tare da mika goron gayyata ga Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku domin yi masa tambayoyi.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sake jaddada haramta duk wani nau’in hawan Dawaki tare da gargadin cewa duk wanda aka samu yana aikata irin wadannan ayyuka za a hukunta shi da gaske.










































