Yara biyu sun mutu sakamakon turmutsitsin da ya afku a babban filin sallar idi na Gombe ranar Lahadi was da dama sun sami raunuka daban-daban.
An bayyana yaran a matsayin Aisha Salisu Ahmed mai shekaru 4½ da Maryam Abdullahi Gwani mai shekaru 4.
An ce rikicin ya samo asali ne lokacin da jama’a da suke kokarin fita daga wurin.
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, a wata sanarwa dauke da sa hannun babban daraktan hulda da manema labarai na gidan gwamnati, Ismaila Uba Misilli, ya jajantawa iyalan ‘yan matan biyu da suka rasa rayukansu.
Ya ce mutane 22 ne abin ya shafa kuma nan da nan aka kai su asibitoci domin kula da lafiyarsu.
Gwamna Yahaya ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike don bin diddigin al’amuran da suka haifar da aukuwar wannan mummunan lamari da kuma hana faruwar hakan a nan gaba.
A cewar sanarwar, tun da farko gwamnan ya aike da wata tawaga mai karfi karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, Alhaji Abubakar Inuwa Kari, domin su ziyarci asibitocin da wadanda abin ya shafa ke karbar magani domin jajanta musu tare da tabbatar da cewa wadanda abin ya shafa sun samu kulawar da ta dace.
A duk wuraren da aka ziyarta da suka hada da asibitin Zainab Bulkachuwa da asibitin kwararru da asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya Gombe, an ga akasarin majinyatan suna cikin koshin lafiya, inda likitoci suka tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba za a sallame su, kamar yadda sauran majinyatan da suka samu raunuka suka yi jinya kuma aka sallame su kafin ziyarar tawagar.
Gwamnan ya bayar da umarnin cewa duk wani kudin jinya ga wadanda abin ya shafa gwamnatin jihar za ta biya domin samar da walwala da samun lafiya tare da saukewa iyayensu duk wani nauyi na kudi da ya shafi kula da ‘yan uwansu.