Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC), a taronta na uku a ranar Litinin, ta amince da bayar da lasisi ga jami’o’i 11 masu zaman kansu a kasar nan.
Ministan Ilimi Dr Morufu Alausa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati bayan kammala taron na majalisar zartarwa FEC.
Ya ce jami’o’in da aka amince da su sun hada da: Jami’ar New City University, Ayetoro da ke Ogun, da Jami’ar Fortune, Igbotako a Jihar Ondo, da Jami’ar Eranova, Mabushi, da jami’ar Minaret Ikirun a jihar Osun sai kuma jami’ar Abubakar Toyin Oke-Agba a jihar Kwara.
Karin karatu: Jami’ar tarayya Kashere ta rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa da Jami’ar Beaconhouse, Pakistan
Sauran su ne: jami’ar Southern Atlantic Uyo a jihar Akwa Ibom da Jami’ar Lens, Ilemona a jihar Kwara;l, da Jami’ar Monarch, Iyesi-Ota a jihar Ogun sai jama’ar Tonnie Iredia a Benin da jami’ar Isaac Balami a jihar Lagos da jami’ar Kevin Eze Mgbowo a Jihar Enugu.
Alausa ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta himmatu wajen fadada harkokin ilimi da ababen more rayuwa, don haka ne ma ta amincewa da sabbin jami’o’in. (NAN)