Yadda WOFAN ke samar da ayyukan yi ga masu bukata ta musamman a Kaduna

WhatsApp Image 2024 12 09 at 18.45.18 1 750x430

A wani yunkuri na samar da ayyukan yi ga masu bukata ta musamman, kungiyar WOFAN ta kaddamar da wani sabon shiri a karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna.

Shirin na nufin samarwa da masu bukata ta musamman sama da 90 aiyuka mai dorewar domin su dogara da kansu.

SolaceBase ta bayar da rahoton cewa, da farko, WOFAN ta tallafa wa nakasassu guda tara da ke gudanar da sana’o’i daban-daban kamar cajin waya, gyaran waya, dinki, gyaran gashi, walda, kera, da sauran sana’o’i.

Wadannan mutane yanzu suna da alhakin horar da ƙarin PWDs guda 10 kowanne a cikin ƙwarewarsu na musamman, domin haɓaka tasirin tattalin arziki na shirin da kuma inganta dogaro da kai a tsakanin masu bukata ta mussaman.

A taron kaddamar da shirin da aka gudanar a karshen mako, shugabar kungiyar WOFAN, Dakta Salamatu Garba, ta bayyana kudirin kungiyar na samar da ‘yancin cin gashin kai ga masu bukata ta musamman.

Ta bayyana cewa shirin na cikin shirin WOFAN ICON-2, tare da hadin gwiwar shirin “Zamu Iya Aiki” na gidauniyar Mastercard, wanda ke da nufin karfafa nakasassu miliyan daya a fadin kasashen Afirka bakwai.

Dr Garba ta kara da cewa “Wannan aikin ya yi dai-dai da dabarun samar da ayyukan yi na Matasan Afirka na Mastercard Foundation, wanda ke neman samar da ayyukan yi masu inganci ga matasa miliyan 30 a Afirka nan da shekarar 2030,” in ji Dokta Garba.

A matsayin wani ɓangare na shirin, kowane kungiyoyin na masu bukata ta musamman zasu sami ₦ 1,050,000 a ƙarƙashin tsarin haɗin gwiwa na  multipurpose cooperative.

Kungiyar mai zaman kanta ta kuma rarraba babura tara da kuma kekuna guda goma ga PWDs.

WhatsApp Image 2024 12 09 at 18.45.18 650x366

Hakazalika WOFAN ta gina cibiyoyin mata uku a Auchan, Kunkumi, da Sayasaya. Wadannan cibiyoyi sun hada da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da ke samar da ruwa mai tsafta ga muhimman wurare kamar asibitin yankin, makaranta, masallaci, da sauran wuraren jama’a. Wannan ci gaba mai dorewa yana tabbatar da samar da ruwa ba tare da katsewa ba.

WhatsApp Image 2024 12 09 at 18.45.20 573x430

 

Mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, wanda Wagon Zazzau, Alhaji Salihu Abubakar ya wakilta, ya yaba da yadda WOFAN ta himmatu wajen tallafa wa marasa galihu.

“Kokarin WOFAN yana da ban mamaki. Muna alfahari da ayyukanku kuma za mu ci gaba da tallafa wa ayyukanku,” in ji shi.

Hajiya Habiba Ibrahim, shugabar nakasassu a karamar hukumar Ikara, ta nuna matukar jin dadin ta ga yadda WOFAN ke kawo sauyi a rayuwa masu bukata ta musamman.

“Wannan shiri zai samar da guraben aikin yi ga nakasassu, wanda shine wani abu da muke kima da gaske,” in ji ta.

Ta jaddada cewa a karshen shirin, sama da nakasassu 90 za su samu ayyukan yi masu inganci, wanda zai ba su damar gudanar da rayuwa mai mutunci da kuma kawar da barace-barace a kan tituna.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin mai suna Dalhatu Abdulhamid wanda ya karbi babur mai amfani da hasken rana kan sana’arsa ta cajin waya, ya bayyana jin dadinsa tare da daukar alkawarin horar da nakasassu guda goma.

“WOFAN ta gyaran cibiyar caji dina da hasken rana da sauran kayan aiki. A yanzu haka sana’ata ta ci gaba, kuma na himmantu wajen koyar da wadannan ’yan’uwa goma duk abin da suke bukata su sani,” in ji Abdulhamid.

Hakazalika, Wasila Yahaya, kwararriyar gyaran gashi ta godewa WOFAN bisa wannan dama da ta ba su, ta kuma sha alwashin horar da dalibai goma a karkashin kulawarta.

Dangane da kokarin shugabar kungiyar WOFAN, Sarkin Jamfalan, Alhaji Aminu Muhammad Bello, wanda Malam Ibrahim Aminu ya wakilta, ya ba Dr. Salamatu Garba lambar girma ta Garkuwar Matan Jamfalan (Mai kare mata a Jamfalan). Bugu da kari, Sarkin Auchan, Alhaji Hassan Lawan, shima ya bata ya bata lambar yabo  saboda irin gudunmawar dake bayarwa ga al’ummar Auchan.

Wannan yunƙurin shaida ne na sadaukarwar da WOFAN ta yi don ɗaga al’umma masu rauni da kuma haɓaka ci gaban tattalin arziki mai ma’ana a Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here