Ambaliyar Ruwa Ta Katse Titin Kano Zuwa Maiduguri

Flood 594x430

Ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama ya janyo katse wani muhimmin bangare na babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri a unguwar Malori-Guskuri dake karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi.

An tattaro hakan ya sa hanyar ba ta iya wucuwa, lamarin da ya tilasta wa masu ababen hawa yin amfani da wasu hanyoyin.

Da yake jawabi a wurin taron a ranar Alhamis, gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya jaddada mahimmancin hanyar, wadda ke zama muhimmiyar hanya tsakanin yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Gwamnan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta gyara bangaren hanyar da ta lalace domin saukaka zirga-zirgar kayayyaki da mutane domin amfanin ‘yan kasa baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here