Harda Aljanu a Zanga-zangar Kano – Dakta Kachako

1723300649822

Babban malamin addinin musuluncin nan wanda yai fice wajan aikin cire aljanu daga cikin bil’adama, Dakta Maigida Kachako, ya ce aljanu  sun shigar zanga-zangar lumanar da aka gudanar a jihar Kano.

Dakta  Kachako wanda tsohon mataimakin kwamadan Hisbah ne ya bayyana hakan ne ranar Asabar ya yin zantawarsa da manema labarai a Kano.

Kachako ya ce su ma aljanu matsin rayuwar ya shafe su, domin daga cikin manyan abincin aljanu akwai kashi, wanda bil’adama ke yarwa bayan sun gama cinye naman dake jiki, wanda shi ma kashin ya yi karanci saboda bil’adama basa cin nama akai-akai sakamakon matsin rayuwa da ake fuskanta a Nijeriya.

Ya kara da cewa hakan ya tillasta wa aljanu shiga sahun bil’adama wajen gudanar da zanga-zanga domin kawo sauyin da zai sa su samin abinci.

Ko da aka tambayi Dr Kachako, ta wacce hanya ya yi magana da aljanun har ya san zasu shiga zanga-zangar, ya ce, sun yi magana da aljanin da ya fada masa hakan ne yayin da yake wa wata mara lafiya rukiya inda aljanin ya tabbatar masa da cewa su ma za su shiga zanga-zanga a jihar Kano.

“Kuma tun da na yi rukiyar aljanin ya fita ya bar ta, ka ga ba sai na dawo da shi ba don ya ba ni labarin yadda suka shiga zanga-zangar. Ni ba labarin shigarsu zanga-zangar ya dame ni ba illa samun lafiyar wanda na yi wa rukiyar. Amma dai (aljanin) ya gaya mun cewa za su shiga zanga-zangar kuma na ce masa to su ji tsoron Allah.

Lokacin da nake tambayarsa me ya sa ya shiga jikinta ya sa mata ciwon kai da sauransu, sai ya ce shi yanzu ma zai bar jikinta domin za su je su shiga zanga-zanga. Na ce masa kun shirya? Ya ce eh, na ce kuna da yawa? Ya kara da cewa eh, sai na ce masa to muna muku nasiha ku ji tsoron Allah, ka ji yadda abin yake.”

Har ila yau, Dr Kachako ya kara da cewa, bisa yadda zanga-zangar ta kasance da cincirindon jama’a da yadda akayi ta’ali na rashin hankali ya nuna akwai nau’in aljanu daban-daban da suka shiga cikin. Yana mai bayyana cewa duk wanda ya san tarihin Musulunci ya san aljanu sun shiga yaki na taimakon addini a zamanin magabata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here