Shugaban kasa Bola Tinubu tare da uwargidansa Oluremi Tinubu sun dawo Lagos da safiyar Juma’a bayan kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu zuwa ƙasar Birtaniya.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa jirgin shugaban kasa ya sauka a bangaren shugaban kasa na filin jirgin sama na kasa da kasa na Murtala Muhammed da ke Lagos da misalin karfe 1:15 na dare.
Jami’an gwamnati manya ne suka tarbi shugaban kasa, ciki har da mataimakin gwamnan jihar Lagos, Dakta Obafemi Hamzat, da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Mista Femi Gbajabiamila.
Sauran sun hada da matar gwamnan jihar Lagos, Hajiya Ibijoke Sanwo-Olu da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC.
Ana sa ran Tinubu zai gudanar da bikin Eid-el-Fitr a Lagos kafin ya koma Abuja domin ci gaba da ayyukan gwamnati a fadar shugaban kasa.
A yayin wannan muhimmiyar ziyara ta Birtaniya, an karbi Tinubu da uwargidansa ta hanyar liyafar sarauta da Sarki Charles na uku da Sarauniya Camilla suka shirya a Windsor Castle.
Shugaban kasar ya kuma gudanar da tattaunawar kasashen biyu da firaministan Birtaniya Keir Starmer a Downing Street a yayin wannan ganawa ta manyan jami’ai.
Kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi na fahimtar juna da suka shafi bunkasa tashoshin jiragen ruwa da hadin gwiwar kasuwanci domin kara karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Najeriya da Birtaniya.
NAN ta rawaito cewa Tinubu ya bar Abuja ranar Talata zuwa London domin ziyarar aiki bisa gayyatar gwamnatin Birtaniya.













































