Mutane da dama daga cikin musulmi sun taru a ranar Juma’a a fadar Nassarawa da ke Kano domin gudanar da sallar Eid-el-Fitr karkashin jagorancin Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda ke nuna karshen watan azumin Ramadan.
An gudanar da sallar ne karkashin jagorancin Sarkin Malamai, Malam Kamalu, wanda ya gabatar da huduba mai mayar da hankali kan ibada, hadin kai da kuma alhakin tarbiyya a tsakanin musulmi.
A cikin hudubarsa, malamin ya bayyana muhimmancin sallar Eid, inda ya bukaci musulmi su kara dankon zumunci, su yi bukukuwan cikin tsari, tare da rungumar yafiya a tsakaninsu.
Ya kuma bukaci al’umma da su rika tuna Allah a rayuwarsu ta yau da kullum tare da inganta hulda da juna, yana mai cewa rayuwa gajeriya ce kuma dole ne a shirya lahira ta hanyar ayyukan alheri.
Malamin ya kuma ce, mutuwa dole ce ga kowa, don haka ya kamata muminai su rayu cikin biyayya ga Allah a kowane lokaci tare da shirya fuskantar ta ta hanyar aikata nagarta.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa malamin ya kuma jaddada bukatar hadin kai a tsakanin musulmi tare da kira ga kowa da kowa da ya hada kai wajen tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma, tare da kauce wa bambance-bambancen siyasa musamman a wannan lokaci na bukukuwa.
Sallar Eid ta ba da damar yin nazari, sabunta imani da kuma kara dankon zumunci a tsakanin musulmi a jihar Kano.













































