Kungiyar mata manoma ta WOFAN ta yi kira ga ‘yan jarida da su rika yada labarai na kishin kasa da sanin ya kamata domin tallafawa kokarin samar da abinci da zaman lafiya a Najeriya.
Kungiyar ta yi wannan kira ne a wajen taron wuni guda na kasa da ta shirya kan inganta samar da abinci, zaman lafiya da dabarun aikin gona dom aka gudanar a Abuja ranar Laraba.
Taron ya samu halartar shugabannin gargajiya, kwararrun yan jaridu, masu bincike kan harkokin noma, da sauran kungiyoyin ci gaban Al’umma, kuma an tattaunan kan rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen magance rikice-rikicen da suka shafi rashin tsaro a fannin noma.

Da take jawabi a wajen taron, shugabar kungiayar Dr. Salamatu Garba ta jaddada bukatar hada kai domin tunkarar kalubalen ƙarancin abinci. “Muna nazarin dangantakar da ke tsakanin samar da zaman lafiya, da karancin albarkatun da ke da alaka da yanayi, da kuma yadda magance wadannan matsalolin
Dokta Salamatu ta jaddada muhimmancin da harshe ke takawa wajen magance rikice-rikice, inda ta bukaci ‘yan jarida da su sake yin la’akari da ka’idojin da za a bi wajen kawo rahotannin rikicin manoma da makiyaya.
Har ma ta bayar da shawarar a sauya laƙabin da ake yiwa makiyaya, ta yadda za a rika kiran su “manoman dabbobi” kwatankwacin yadda ake kiran manoman amfanin gona.
“Maimakon mu kira su makiyaya, shin za mu iya kiran su a matsayin manoman dabbobi ko kuma masu kiwon kaji? kamar yadda muke kiran manoman masara da shinkafa? Wannan sauyin harshe na iya zama mafarin inganta zaman lafiya da rage tashin hankali tsakanin al’umma,”.
Ta kuma jaddada mahimmancin samar da jin dadin ‘yan jarida da walwalar su, inda ta nuna cewa da yawa suna aiki a cikin mawuyacin hali ba tare da samun kariya ba, inda ta yi kira da a samar da tsarin inshora ga kwararrun kafafen yada labarai da suke yada labaran da suka shafi tsaro don tabbatar da tsaron lafiyarsu yayin tattara labari da yada shi.
Da take bayani kan rawar da shugabannin gargajiya ke takawa wajen samar da zaman lafiya Dakta Salamatu Garba ta bayyana cewa, ya kamata shugabannin al’umma a matsayinsu na masu kula da al’adun gargajiya da gudanar da harkokin mulki na gari, su ba da himma wajen ganin an magance tashe-tashen hankula tsakanin manoma da masu kiwo. “Shugabannin gargajiya ne suke fara sanin lokacin da baƙin mutane suka shigo cikin al’umma, kuma galibi su ne ke da alhakin sasanta rigingimu, don haka ba za a yi watsi da rawar da suke takawa wajen warware rikici ba,”.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa, taron tattaunawar WOFAN-ICON2 ne ya shirya a kasa, wanda Gidauniyar Mastercard ta tallafa tare da hadin gwiwar ma’aikatar aikin Gona da tsaro ta Tarayya da ma’aikatar kasafin kudi da tsare- tsaren tattalin Arziki ta tarayya, da Cibiyar binciken hatsi ta kasa, Badeggi, da Cibiyar Albarkatun Kasa ta HEDA, UN-POLAC, NAERLS, da jaridar SolaceBase da Gidan Rediyon Express.
Shirin WOFAN-ICON2 shiri ne na tsawon shekaru biyar da gidauniyar Mastercard ke tallafawa, wanda ke da nufin karfafa gwiwar manoma dubu 675,000 da kuma karfafa wadatar abinci a Najeriya.

A nasa bangaren, shugaban babban taron majalisar dinkin duniya (UNGA) karo na 74, kuma tsohon shugaban jami’ar Uthman Dan fodio dake Sokoto, Farfesa Tijjani Muhammad Bande, ya yaba da shirin na taron tattaunawa na kasa, inda ya jaddada bukatar samar da abinci mai gina jiki tare da cimma muradun ƙarni mai lamba ta 2 na kawo karshen yunwa nan da shekarar 2030.
Ya ce hanyar shigar da manyan masu ruwa da tsaki a matsayin abokan hadin gwiwa a wannan tafiya na neman mafita mai dorewa kan rikicin manoma yana da matukar muhimmanci, sai da ya roki taron da ya samar da shawarwari masu dacewa don magance rikicin manoma da makiyaya.
Farfesa Bande ya yaba da tsarin shigar da kafafen yada labarai a matsayin mahalarta, ba wai kawai su dauki labaran don su sanar da jama’a ba, sai don su ma su bada tasu gudunmawa.
Shi ma mataimakin shugaban cibiyar inganta Rayuwa ta majalisar dinkin Duniya (UN-POLAC), Farfesa Joseph Legend, yayin da yake bayyana hanyar samar da zaman lafiya, ya ce, shirya tarukan tattaunawa ne kaɗai mafita, da kuma kulla alaka da sauran taruka irin su.
Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta ƙasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, ya bayar da tabbacin cewa ‘yan jarida za su bayar da gudunmawar su wajen inganta rahotanni da kuma samar da al’umma muhimmancin zaman lafiya a Najeriya.
“Ina so in yi amfani da wannan dama domin in yaba wa WOFAN bisa hadin gwiwar da ta yi a wannan muhimmin lokaci. Wannan kuma lokaci ne na tunatar da kanmu muhimmiyar rawar da muke takawa a matsayin masu ruwa da tsaki wajen inganta zaman lafiya da ci gaba. Ina tabbatar muku da cewa muna samun gagarumin ci gaba wajen cimma manufofinmu guda,”.
Ya jaddada cewa samun dauwamammen zaman lafiya a Najeriya na bukatar cikakken aiwatar da kudurin majalisar dinkin Duniya na 1925. “Wannan kuduri da Najeriya ta amince da shi a shekarar 2000, ya nuna muhimmancin shigar mata cikin harkokin bada shawarwari da kokarin samar da zaman lafiya. Tabbatar da shiga cikin waɗannan ayyukan zai ba da gudummawa sosai ga kwanciyar hankali da ci gaba mai dorewa. Sannan kafofin yada labarai na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tsara maganganun da jama’a za su saurara da kuma tabbatar da cewa an kiyaye ka’idoji. Ina kara jaddada kudurinmu na hada kai don cimma wadannan manufofin.”
Ya kuma jaddada aniyar kungiyar ta NUJ a kan muhimman batutuwa guda biyu: kishin kasa da kuma kwarewar aikin jarida. “Don mu gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata a matsayinmu na ‘yan jarida, muna bukatar kasa mai zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ta hanyar yin aiki tare, za mu iya tsara ingantaccen labari tare da ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban ƙasa,” a cewar Alhassan.
A nasu jawaban, Etsu Kwali shugaban majalisar Gargajiya ta Kwali, Luka Ayedoo Nizassan sun yabawa babbae darakta ta WOFAN bisa kokarinta na ci gaba da gudanar da ayyukan da ke amfanar ‘yan Najeriya. “Ina so in yi amfani da wannan dandali domin taya shugabar kungiyar WOFAN murna, domin tana yin wani aiki wanda ya kamata ace gwamnati ta jagoranci yin sa”.
Etsu Kwalli ya jaddada alakar da ke tsakanin samar da abinci, bunkasar tattalin arziki, yawan amfanin gona da zaman lafiya. “Idan daya daga cikin wadannan sassan ba su kyautata ba, yana shafar dukkanin wani tsarin gaba daya. Shi ya sa wannan taro ke da matukar muhimmanci kuma yazo a kan lokaci. Noma a Najeriya ya ba da gudummawar kashi 25.75 cikin 100 wajen samar da aikin yi a shekarar 2024 kuma yana da matukar tasiri ga bunkasar tattalin arzikin mu na GDP. Duk da haka, guraben aikin yi a aikin gona na raguwa, kuma gudummawar da take bayarwa ga GDP ta tsaya cik saboda tashe-tashen hankula, sauyin yanayi, da sauran manyan kalubale. Dole ne mu dauki matakan da suka dace don magance wadannan matsalolin.”
A karshe ya jaddada kudirin shugabannin gargajiya kan wannan batu. “Idan GDP namu ya girma a zahiri, kowa zai amfana. Ci gaban tattalin arziki da rage talauci suna tafiya kafada da kafada. A madadin sarakunan gargajiya, ina so in tabbatar muku da cewa muna cikin wannan harka, kuma za mu ba da gudummawar mu da cikakken goyon baya da jajircewarmu.”













































