Jami’an tsaro sun kubutar da ‘yan uwan Nabiha da aka yi garkuwa da su

Najeebah 750x430

Rundunar ‘yansandan kasar nan ta ce jami’anta sun kubutar da sauran ‘yan mata biyar ‘yan uwan Nabeeha da aka kashe.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar tace ta kubutar sauran yan matan ne a wani samame da suka kai a kusa da dajin Kajuru da ke Kaduna da misalin karfe 11:30 na daren Asabar, 20 ga watan Janairu.

Karanta wannan: Daukar Yan sanda: Mun tantance masu neman aiki sama da dubu 136-PSC

Sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yansandan birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh ta fitar ta bayyana cewa: “Bayan matsa kaimi na sashen yaki da satar mutane na rundunar ‘yansanda tare da hadin gwiwa da jami’an sojin Najeriya game da harin da masu garkuwa da mutane suka kai kan unguwar Zuma 1 na yankin Bwari a ranar 2 ga watan Janairun 2024, ‘yansandan yankin Birnin Tarayya sun samu nasarar ceto wadanda abin ya rutsa da su.”

Sanarwar ta kara da cewa “tuni aka hada su da ‘yan’uwansu.”

Sai dai sanarwar ba ta yi karin bayani kan ko an yi artabu tsakanin jami’anta da masu garkuwa da mutanen ba ko kuma a’a.

Karanta wannan: Gobara ta Lalata kasuwar Panteka dake Kaduna

A ranar Talata 2 ga watan Janairu, 2024 ne ƴan fashin daji suka auka gidan su Nabeeha suka sace ta tare da mahaifinta da ƴan ‘uwanta mata biyar.

Daga bisani suka saki mahaifinta domin ya kawo kudin Fansa, lamarin ya kuma kai ga kashe Nabeeha saboda gaza cika wa’adin biyan kudin fansa.

Lamarin da ya jima yana ci wa al’umomi da dama musamman a arewacin ƙasar tuwo a ƙwarya, duk da yunƙurin da hukumomi suka ce suna yi na magance shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here