Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kasa PSC ta ce daga lokacin da aka fara aikin tantance masu neman shiga Dan sanda a ranar 8 ga watan da muke ciki na Janairu zuwa yanzu an tantance mutanen da basu gaza 136,177 ba.
Mai magana da yamun hukumar Ikechukwu Ani, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.
Karanta wannan: Gwamnatin tarayya ta sake yin alkawarin kammala titin Abuja zuwa Kaduna a wannan Shekara
Yace ya zuwa yanzu an dora jimullar wadanda aka tantance dubu 108, 768 a shafin Internet.
Ya kara da cewa sauran wadanda ba dora ba hakan ya faru sakamakon matsalar sadarwa.
Karanta wannan: Jihar Yobe: Buni ya nada Kole Shettima da wasu mutane 23 a matsayin masu bashi shawara
Hukumar ta hannun sashen kula da daukar aiki yanzu haka tana tsaka da tantance matasan Kasar nan da ke sha’awar shiga aikin su dubu 416,270.