‘Yan Majalisu sun bukaci a dakatar da Alkalan Kotun daukaka kara

'yan majalisu
'yan majalisu

Tawagar Majalisar wakilai ta bukaci alkalan kotun daukaka kara da su kakaba mata takunkumi kan tsige ‘yan majalisar jihar Filato.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai Chinda Kingsley ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.

Ya ce ya kamata a tsawatar da alkalan da suka gudanar da shari’ar domin su zama tamkar hana wasu alkalan da za su so su bi irin wannan hanya a nan gaba.

Karanta wannan: Sojoji sun kama wasu dilolin kwaya a Ogun tare da kin karbar cin hancin miliyan 12

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, a watan Nuwambar 2023, ta kori dukkan ‘yan PDP 16 a majalisar dokokin jihar Filato, saboda al’amuran da suka shafi tunkarar zaben.

Hakan ya yi iyaka da zargin rashin bin umarnin kotu da rashin tsarin siyasa, kafin wannan lokacin dai kotun daukaka kara ta kori ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar PDP hudu daga jihar da wasu sanatoci biyu.

Karanta wannan: Tinubu ya amince da sakin Naira Biliyan 3 don tabbatar da tantance Rajistar ‘yan kasa

Kingsley ya kuma taya jam’iyyun adawa murna kan hukuncin da kotun koli ta yanke na maido da nasarar da gwamnonin adawa suka samu da kotun koli ta tabbatar da nasararsu.

Kazalika ya bayyana sunayen gwamnonin da suka hada da Dr. Alex Otti na Abia, Fasto Umo Eno na Akwa Ibom, da Sen. Bala Mohammed na jihar Bauchi, da Alhaji Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.

Sauran sun hada da Mista Caleb Mutfwang na jihar Filato da kuma Mista Lawal Daudu na jihar Zamfara.

Karanta wannan: Daukar Yan sanda: Mun tantance masu neman aiki sama da dubu 136-PSC

Kingsley ya ce, “Muna yaba wa alkalan kotun koli da suka tabbatar da cewa ba’a tauye hakkin kuri’un mutanen wadannan jihohin ba.

“Wadannan hukunce-hukuncen sun sabunta imanin ‘yan Najeriya a fannin shari’a domin ya nuna cewa shi ne fata na karshe na talaka.”

Ya ce nasarorin da aka samu ba wai ga jam’iyyun adawa kadai ba ne, har ma da ‘yan jihohin da suka zabi jam’iyyar PDP da LP da kuma NNPP masu dimbin yawa.

Ya ce ya zama wajibi a yi la’akari da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan zabukan ‘yan majalisar jiha da na ‘yan majalisun tarayya da aka yi a Filato da ya kori ‘yan majalisar PDP da dama bisa wasu dalilai da ake tantama.

Karanta wannan: Gobara ta sanya Mutane 120 rasa gidajen su a Ilorin

Ya kara da cewa wadancan dalilai da kotun koli ta yi amfani da su wajen ajiye hukuncin a gefe, ba za’a iya daukaka kara a kan hukunce-hukuncen da aka yanke ba saboda sun haifar da rashin adalci.

Ya ce ya kamata a tsawatar da alkalan da suka mika su domin su zama masu hana sauran alkalan da za su so su bi wannan tafarki nan gaba.

Kingsley ya ce kungiyar ta yabawa gwamnonin jam’iyya mai mulki da aka dawo da su tare da yi musu fatan alheri kamar yadda NAN ta rawaito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here