Yajin aikin Malamai a Abuja: Wike ya zargi shugabanin kananan hukumomi

Wike 5
Wike 5

Ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike, ya zargi shugabanin kananan hukumomi 6 akan yajin aikin da Malaman Firamare ke yi yanzu haka a Abuja.

Wike wanda ya yi magana da manema Labarai gabanin Shiga wata ganawar sirri ta gaggawa da hukumomin tsaro da kuma shugabanin kananan hukumomi ranar Talata a Abuja, yace shugabanin kananan hukumomin ba sa gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

Karanta wannan: NiMet ta yi hasashen cewa za a yi gagarumin ruwan sama a jihohin arewa 6 ciki harda babban birnin tarayya Abuja

Kamfanin dillancin Labarai NAN ya rawaito cewa tun a ranar Lahadi ne kungiyar Malaman makaranta reshen babban birnin tarayya ta umarci Malaman Firamare da su shiga yajin aikin sai Baba ta gani daga ranar 15 ga watan Janairu.

Yajin aikin wanda ci gaban na baya da kungiyar ta dakatar ne tun a shekarar da ta gabata ta 2023, wanda ta shiga akan kin mambobin ta kaso 40 cikin 100 na alawu-alawus da biyan bashin mafi karancin albashi har na tsawon watanni 25 da sauran batutuwa.

Karanta wannan: Muna samun ci gaba a yaki da miyagun laifuka-Gwamnatin Katsina

A ranar 2 ga watan Oktoban shekarar 2023 ne kungiyar ta janye yajin aiki, domin bawa mahukunta damar kamo bakin zaren matsalalolin cikin makwanni 6, sai dai har kawo yanzu babu wani sauyi.

Ministan ya zargi shugabanin kananan hukumomin akan yajin aikin inda kuma ya bukace su da su mayar da hankali akan ayyukan su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here