Hotuna: Ɗimbin jama’a sun tarbi Sarki Aminu bayan ziyarar da ya kai Abuja

WhatsApp Image 2024 08 27 at 23.38.59 750x430

A ranar Talata ne Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya dawo Kano bayan ziyarar kwanaki biyar da ya kai Abuja, inda ya halarci wasu tarurruka.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa, bayan isowarsa filin jirgin saman Malam Aminu Kano ya samu gagarumar tarba daga masu rike da mukaman gargajiya da wasu mukarrabansa da dimbin magoya bayansa da suka taru a filin jirgin domin tarbar sarkin.

WhatsApp Image 2024 08 27 at 23.38.57 768x512

Jirgin mai zaman kansa da ya kawo sarki Aminu Bayero ya sauka daidai karfe 3:30 na rana. Magoya bayan sun jera ayarin motocin da suka raka Sarki na 15 daga filin jirgin zuwa karamar fadar Nasarawa.

WhatsApp Image 2024 08 27 at 23.39.00 768x509

WhatsApp Image 2024 08 27 at 23.38.59 768x509

WhatsApp Image 2024 08 27 at 23.39.04 768x509

 

 

Idan dai za a iya tunawa, tafiyar ta kasance karo na farko da Alhaji Aminu Ado Bayero ya fita daga Kano tun bayan rikicin masarautu a ranar 23 ga watan Mayun bana inda gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sake nada Malam Muhammad Sanusi II.

Haka kuma, Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II ya iso ne a makon da ya gabata daga kasar Birtaniya inda ya kare karatunsa na digiri na uku watau PhD, kasancewarsa na farko da ya yi balaguro daga jihar tun farkon rikicin.

WhatsApp Image 2024 08 27 at 23.39.08 768x512

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here